- Dakarun Sojin Najeriya sunyi nasarar kama wani babban kwamandan kungiyar Boko Haram tare da halaka wasu yan ta'addan da dama
- Sun kama shi a wani samame da dakarun atisayen 'Deep Punch' suka kai a dajin na Sambisa
- Dakarun sojojin sun sun kwato kayayaki da suka hada da babura, tutar Boko Haram, na'urar samar da wuta, hatsi, katifa, injinan nika, da rumbun ajiyar na karkashin kasa

Dakarun Sojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram biyar kuma sunyi nasarar kama wani babban kwamandan kungiyar a atisayen 'Deep Punch II' ta rundunar ke gudanarwa a dajin Sambisa da kuma tafkin Chadi kamar yadda hukumar sojin ta sanar.

Mataimakin Direkta kuma mai magana da yawun hukumar sojin, Kwanel Onyeama Nwachukwu ne ya bayar da sanarwan a garin Maiduguri. Sanarwan har ila yau ta ce dakarun sun ceto mutane uku, motocin hawa da kuma muggan makamai iri daban-daban a cikin kwanakin biyu da suka wuce.

Mista Nwachukwu yace a ranar Alhamis, Dakarun sojin sunyi artabu da wasu mayakan kungiyar ta Boko Haram a yayin da suke kokarin tserewa daga kawanyar da sojojin sukayi musu a wani yanki mai suna 'Sabil-Huda' da ke dajin na Sambisa.

Mista Nwachukwu ya kara da cewa a ranar Juma'a Dakarun Sojin sun kai samame a sansanin 'Camp Zero' inda suka halaka yan ta'addan da dama duk da illar da bam din da yan ta'addan suka birne a kasa tayi wa motar yakin na sojojin.

Hakazalika, Nwachukwu ya sanar da cewa dakarun bataliya 151 tare da hadin gwiwan '7 Div' sunyi nasarar ruguza sasanin yan ta'adda guda tara a yankin Frigi-Izza, sun kwato kayayaki da suka hada da babura, tutar Boko Haram, na'urar samar da wuta, hatsi, katifa, injinan nika, da rumbun ajiyar na karkashin kasa.