Dakarun sojin Najeriya sun kama wani kasurgumin dan bindiga dan Fulani a karamar hukumar Guma na jihar Benuwe, garin da ake yawan samun tashin tshina a jihar, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito. Majiyar NAIJ.comta ruwaito sunan dan bindigan Idi Gemu, sa’annan sun kama bindigarsa kirar AK 47, wannan kamen ya kawo adadin yan bindigar da Sojoji suka kama a karamar hukumar Guma zuwa hudu.

Kwamandan rundunar Soji ta 72, Laftanar Kanal Suleiman Mohammed ya sanar da kama Idi Gemu a ranar Laraba 2 ga watan Mayu, inda yace sun kama Dan bindigan ne a ranar Talata 1 ga watan Mayu.

Kanal yace a ranar 26 ga watan Mayu Sojoji sun kama yan bindiga guda uku, inda yace sakamakon binciken yan bindigan ne suka samu bayanan da suka kai su ga kama Idi Gemu, ya kara da cewa rundunar zata cigaba da kawar da duk wani barazanar tsaro don tabbatar da kare dukiya da kare rayukan al’aumma. Sai dai Gemu ya bayyana ma manema labaru cewa bindigar da aka gani a hannunsa ba nasa bane, na wani abokinsa ne da ya tsere a lokacin da ya hangi Sojoji, yayin da shi yake kwance yana bacci.