Majiyarmu HausaM ta yi kokarin kawo muku wani binciken masana da suka gabatar wanda ke nuna jerin kasashen duniya guda biyar wadanda suka fama da kuncin rayuwa da kuma kasashe guda biyar wadanda suke cikin jin dadin rayuwa A cikin mutane dubu dari da hamsin da aka yi zance da su a kasashen duniya fiye da dari da arba'in, kusan kashi daya cikin uku sun bayyana cewa suna zaune cikin matsin rayuwa, inda mutum daya cikin kowanne mutane biyar suke bayyana cewa suna fama da matsanancin fushi da bacin rai a rayuwarsu. A rahotannin da majiyarmu HausaM ta samu ya nuna cewa kasar Chadi ita ce kasar da ta fi kowacce kasa shiga halin kaka-ni-ka-yi, daga ita kuma sai kasar Nijar wacce ta ke biye mata. Kasar Paraguay kuma ita ce kasar da ta fi kowacce kasa a duniya jin dadin rayuwa. Kasar Amurka kuma ita ce ta 39 cikin kasashen da suka fin jin dadin rayuwa a duniya, sai kasar Birtaniya wacce ta ke a matsayi na 46, kasar Indiya kuma ta na matsayi na 93. Masanan sun fi mayar da hankalinsu akan mutane masu fadi tashi, wadanda ake tambaya sai sunyi kwana daya kafin su yi nazari akan tambayar. Masanan sun gano cewa mutanen sun shiga matsin rayuwa sosai. Kashi 39 na mutanen da aka tambaya sun ce shiga damuwa sosai kafin ayi musu tambayar, kashi 35 kuma sunce sun shiga matsi. Jerin manyan kasashen duniya guda biyar da suka fi jin dadin rayuwa *.Paraguay *.Panama *.Guatemala *.Mexico *.El Salvador Jerin manyan kasashen duniya guda biyar da suka fi yin rayuwar kunci *.Chadi *.Nijar *.Saliyo *.Iraki *.Iran