- Wani Alkali a Garin Kano yayi watsi da tayin cin hancin da aka ba sa
- An yi wa wannan Alkali tayin kudi Miliyan guda don a danne gaskiya
- Sam ba kasafai ake samu masu shari’a da ke da gaskiya irin wannan ba

A jiya mu ka samu wani labari daga Transparency IT Nigeria na wani Alkali a Jihar Kano wanda yayi abin a-yaba inda yayi watsi da tayin cin hancin da aka ba sa domin ya ba canza hukuncin shari’a.

Babban Majistare na wani Kotu da ke Unguwar Rjiyar Zaki a Garin Kano mai suna Aminu Sulaiman Fagge ya ki karbar wannan cin hanci da aka ba shi a kan wata shari’a da ake yi. Aminu Fagge yace hakan cin zarafin shari’a ne.

Wannan Bawan Allah dai ya ki karbar Miliyan guda da aka ba shi domin ya saye goro. A cewar sa ma dai an raina masa wayau ne da aka yi kokarin ba shi cin hancin. Yanzu haka ma mun ji cewa an yi ram da wanda ya kawo masa cin hancin. Ba kasafai dai ake samun irin wadannan masu shari’a ba a Kasar yayin da ake kokarin yaki da rashin gaskiya. Alkalin yana ganin darajar sa ta wuce ya saida ta kan kudi Naira Miliyan daya.