Akalla dalibai yan mata 94 ne suka yi batan dabo tun bayan wani hari da yan ta’addan Boko Haram suka kai a kwalejin yan mata dake garin Dapchi, cikin karamar hukumar Busari a jihar Yobe.

Iyaye da malaman makarantar ne suka tabbatar da batar adadin daliban da a yanzu ba’a san halin da suke ciki ba, ko kuma inda suke ba, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Majiyar 365news ta ruwaito da misalin karfe 7 na daren ranar litinin 19 ga watan Feburairu ne yan ta’addan suka far ma kwalejin yan matan, cikin motocin yaki guda 18, kuma har an gano gawawwakin dalibai hudu a cikin daji.



Har sai bayan da yan ta’addan suka kammala ta’asar da suka yi a kwalejin yan matan ne sai ga Sojoji cikin motocin yaki da jiragen sama masu tashin angulu sun nufo makarantar, ba tare da samun nasarar cimma yan ta’addan ba.

Idan za’a tuna a watan Afrilun shekarar 2014 ne yan Boko Haram suka sace dalibai mata 270 dake karatun a kwalejin sakandarin yan mata dake garin Chibok, inda sai a shekarar 2017 ne gwamatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta amso mata 100 daga cikinsu.