Mun samu labari daga Jaridun kasar nan cewa Ngozi Okonjo-Iweala wanda ita ce Ministar kudi a lokacin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ta bayyana irin wawason da yaran Jonathan su ka yi a lokacin da yake mulkin kasar. Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a wani sabon littafi da ta rubuta game da yaki da sata ta bayyana cewa a Satumban 2011 tayi kokarin a soke tsarin CTN da ke aiki a tashar jiragen ruwan kasar saboda ganin cewa akwai zalunci a tsarin.

‘Yan kasuwa dai sun koka da cewa tsarin na CTN bai da wani amfani illa kurum tatse su da ake yi don haka ta nemi a soke shi. Tsohuwar Ministar kudin tace duk shekara ana samun Dala Miliyan 6 daga tsarin amma ba a ba Gwamnati.

Sai dai tace hakan bai zo mata da sauki ba domin kuwa bayan an soke wannan tsari ne wani da ke kusa da Shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi ta aiko mata da sako cewa ta dakatar da wannan aiki da ta dauko don kuwa yana da illa. A dai littafin na ta, babbar Masaniyar tace wani na kusa da Shugaban kasar ya nemi ta tsaya a ofishin sa Fadar Aso Villa duk lokacin da ta zo domin su yi magana. A dalilin haka dai har sai dai aka hana ta shiga fadar Shugaban kasar. Jiya kun ji cewa wani Hadimin tsohon Shugaban kasa Jonathan Goodluck watau Reno Omokri yayi wa Shugaba Muhammadu Buhari kaca-kaca game da ziyarar Amurkan da Shugaban kasar ya kai jiya.