Amina Mallam Usman mai shekaru 15 a duniya, daya daga cikin dalibar makarantar Dapchi ta jihar Yobe, da mayakan Boko Haram suka kai hari a cikin makon da ya gabata, ta sha da kyar yayin da ta bugi kirji ta kai gardawan maza har kas.

Ita dai wannan daliba ta kubuta ne a yayin da 'yan ta'addan ke cuku-cukun makire motocin su da 'yan uwanta dalibai, inda kamar yadda ta furta ikon Allah ya sanya ta kubuce domin kuwa da taimakon sa ne ta sha.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, 'yan lokuta kadan ne ke tsakanin ta gurbacewar rayuwarta, domin kuwa 'yan ta'adda sun kai mata cafka daban-daban da sa'ar da su taka ita ce kawai yin gaba da hijibin dake sanye a jikin ta.

Daliba Amina ta bayyana cewa, tayi gudun fanfalaki da ba ta taba makamancin sa a rayuwar ta ba, inda ta nemi mafaka a wata rigar Fulani mai sunan Miligia.

Ta ci gaba da cewa, ta so Mala'ikun mutuwa su zare ran jikinta a yayin da ta fuskanci wannan mutane 'yan Boko Haram ne, inda ta yi gudu na tsawon kilomita biyar bayan da mayakan suka kai farmakin dakunan su na kwana.

Ta kara da cewa, ba ta wani buri a rayuwarta da wuce fata da kuma rokon Ubangiji domin ya kubutar da sauran 'yan uwanta dalibai da suke hannun 'yan ta'adda kamar yadda ya kubutar da ita.

Jaridar 365News ta kuma ruwaito cewa, 'yan sanda sun damke wasu mutane biyu da muggan makamai a yayin taron jam'iyyar PDP da aka gudanar a jihar Ebonyi.