Hedkwatan babban bankin Najeriya (CBN) dake Abuja ya kama da wuta. An rahoto cewa wutan ya ara ne da yammacin yau, Talata, 1 ga watan Mayu. A halin yanzu ba’a gano abun da ya haddasa tashion gobaran ba.

Ana nan ana kokarin ganin an kashe wutan sannan kuma babu rahoto akan ko abun ya cika da wani tukuna.