A yau, Litinin, hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ta gurfanar da tsohon ministan wutar lantarki, Muhammad Wakil, da wasu mutane 4 gaban mai shari’a M.T Salihu na babbar kotun tarayya dake Maiguduri bisa tuhumarsu da badakalar kudi, miliyan N341m.

Ragowar mutanen su ne Garba Abacha, Ibrahim Birma, Abubakar Kullima da Muhammad Kachalla. Ana tuhumar Mista Wakil da ragowar mutane hudu da karbar dalar Amurka daga tsohuwar minister man fetur, Diezani Alison-Madueke, domin yakin neman zaben shugaban kasa na 2015.

Dukkan wadanda ake tuhuma sun ki amsa laifinsu.

Lauyan hukumar EFCC, H. A. Shehu ya nemi kotu ta bayar da umarnin tsare wadanda ake zargin a gidan yari. Bukatar da lauyan wadanda ake tuhuma, M. Umoru, ya gaggauta sukanta tare da neman kotu ta bayar da umarnin tsare su a ofishin hukumar EFCC kafin lokacin da za a saurari karar bayar da belinsu.

Mai shari’a Salihu ya daga shari’ar zuwa ranar Talata, 3 ga watan Yuli, domin sauraron bukatar bayar da belin wadanda ake tuhuma.