Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati ta kwace, na wucin gadi, katafaren Otal din biliyan N1bn da wani gida na miliyan N500m daga hannun tsohon kakakin tsohon shugaban kasa Jonathan.

Kazalika hukumar ta EFCC ta kwace wani katafaren gida na miliyan N500m dake unguwar Maitama a Abuja, mallakar wani na kusa da tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki.

Alkalin babbar kotun Abuja ta 10 dake Abuja, mai shari'a Nnamdi Dimgba ne ya bawa hukumar EFCC izinin kwace kadarorin biyu

An kwace Otal din Niboro ne bayan hukumar EFCC ta bankado wasu makudan kudi, dalar Amurka 5.9, da aka bashi daga ofishin Sambo Dasuki domin gyara sunan Jonathan a idon duniya, gabanin zaben shekarar 2015. Hukumar EFCC ta gano yadda Niboro ya aika kudaden zuwa wasu kamfanoni guda biyu dake biranen Washington DC da Chicago a kasar Amurka.

Ko a jiya, Litinin, hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ta gurfanar da tsohon ministan wutar lantarki, Muhammad Wakil, da wasu mutane 4 gaban mai shari’a M.T Salihu na babbar kotun tarayya dake Maiguduri bisa tuhumarsu da badakalar kudi, miliyan N341m.

Ragowar mutanen su ne Garba Abacha, Ibrahim Birma, Abubakar Kullima da Muhammad Kachalla. Ana tuhumar Mista Wakil da ragowar mutane hudu da karbar dalar Amurka daga tsohuwar minister man fetur, Diezani Alison-Madueke, domin yakin neman zaben shugaban kasa na 2015.