- Hukumar tsaron Najeria na jihar Edo, da Civil Defence, da kuma NSCDC sun tabbatar da kama wanda ake zargin da dan zama Boko Haram.
- Dangane da bayanin Shugaban tsaro ta NSCDC, Makinde Ayinla, wanda ake zargin ya ce sunan Sani an kama shi ne a rana Asabar.

Matakan tsaron da aka sanya kula da gida Talabijin wato NTA sun kamashi ne bayan sun ganshi yana ta sintiri a cikin harabar gidan da misalign karfe 2 na dare zuwa karfe 4. Ba wanda ya san yanda akayi a samu hanyar shiga gidan.

Bayan tuhumar sa da akayi Sani ya fadi cewa shi dan kungiyar Boko haram ne.

Mr Ayinla ya ce sani ya fadi cewa yana cikin Kungiyar msu Fashi da Makami, da Garuwa da Mutane, da Sata, da Kisa, da kuma saida Mutane. Sani ya ce kungiyar tasu na amfani da manyan makamai.

Mr Ayinla ya ce bayan an tambayi Sani ko zai iya kai hukumar tsaro wurin da ‘yan uwan nasa suke yace Allah kadai zai iya kai mutun wurin. Kwamandan yace tuni dai sun mika shi zuwa hukumar ‘yan Sandan ciki ta kasa a jihar.